Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Da yake bayani game da batun shirya dafatarin yin aiki tare a mashigar tekun kasfiya a bangaren kimiyya, bincike da ayyukan ceto, da yaki da masu fataucin miyagun kwayoyi da kuma fada hadin guwai tsakanin kasahen yankin, Moradov ya bada shawara a gudanar da taron tsakanin ministocin harkokin wajen kasashen guda biya na mashigar tekun kasfiya domin fadada hanyoyin yin hadin guiwa tsakanin bangarorin biyu
A nasa bangaren ministan wajen kasar iran ya cewa A kowanne lokaci Iran tana maraba da duk wani mataki na fada dangantaka tsakanin musamman a mashigar tekun kasfiya, daga karshe ya taya takwaransa na kasar Turkumanistan farin cikin shiga Azumin wata Ramadana mai alfarma.
342/